Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe makonni huɗu a ƙasashen Turai, a wani hutun aiki da Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa ya tafi gudanarwa.
Jirgin shugaban ya sauka a sashen jiragen shugaban ƙasa na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin ƙarfe 6:22 na yamma ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026.
Tinubu ya bar Abuja a ranar 30 ga Agusta zuwa Landan, inda ya shafe kusan mako guda kafin ya wuce Paris ta ƙasar Faransa.
Daga bisani Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙara masa wasu kwanaki bayan da aka sanar da cewa hutun aikin zai ɗauki makonni uku.
- Tinubu ya bar Paris, zai dawo Najeriya
- Najeriya a shekaru 66: Daga kare iyakoki zuwa yaƙi da sabbin barazanar tsaro
A lokacin zamansa a Paris, Tinubu ya gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wani liyafar cin abinci ta sirri, sannan ya kuma tattauna da wasu shugabannin ‘yan kasuwa, ciki har da Vincent Bolloré na Kamfanin Bolloré Group.
Ana sa ran Shugaban Ƙasar zai ci gaba da zama a Legas domin halartar wasu shirye-shiryen bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya a ranar 1 ga Oktoba.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma ce Tinubu zai gudanar da wasu ayyukan hukuma a Legas kafin daga bisani ya koma Abuja.