Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala hutun aikinsa a Turai, inda ya bar birnin Paris na Faransa domin komawa Najeriya.

Fadar Shugaban Ƙasar ta ce jirgin shugaban ana sa ran zai sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a yammacin Talata.

Tinubu zai fara zamansa a Legas, inda zai halarci bukukuwan cikar Najeriya shekaru 66 da kuma bikin karrama marigayi MKO Abiola a gidan wasan kwaikwayo na Wole Soyinka da ke Iganmu.

Tinubu ya bar Abuja tun ranar 30 ga watan Agusta zuwa Landan domin hutun shekara, kafin daga bisani ya zarce Paris, inda ya gudanar da wasu ganawa da shugabannin kasuwanci da masu zuba jari, ciki har da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Vincent Bolloré.

A lokacin zamansa a Paris, shugaban ya kuma halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi gina katafaren tashar jiragen ruwa a Ogun Waterside da kuma yankin tattalin arzikin Blue Marine, wanda ake sa ran zai jawo sama da dala biliyan 7 na zuba jari.

Fadar Shugaban Ƙasar ta ce Tinubu zai kuma gudanar da wasu ganawa da shugabannin siyasa da abokan hulɗa a Legas gabanin zaɓen 2027, kafin ya koma Abuja bayan kammala harkokinsa a jihar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *