Muƙaddashin Kocin Super Falcons, Augustine Eguavoen, ya zaɓi kyaftin Rasheedat Ajibade, da mai tsaron gida Chiamaka Nnadozie, da ‘yan wasan baya Michelle Alozie da Oluwatosin Demehin, cikin jerin ‘yan wasa 28 don buga wasan neman gurbin shiga Gasar Olympics ta Los Angeles 2028 da za’a buga da Comoros a wata mai zuwa.

An umarci ‘yan wasan da su bayyana a otal din AM2PM da ke Ijebu-Ode a ranar Asabar, 3 ga Oktoba.

Comoros za ta karɓi baƙuncin wasan farko a zagaye na biyu a ranar Jumma’a, 9 ga Oktoba, yayin da Najeriya za ta karɓi baƙuncin wasa na biyu a ranar Talata, 13 ga Oktoba.

Za a buga wasannin biyu a filin wasa na Remo Stars da ke Ikenne-Remo, saboda Comoros ba ta da filin wasa da CAF ta amince da shi don buga wasannin ƙasa da ƙasa.

Idan Najeriya ta samu nasara a wasannin biyu, Falcons za ta samu damar zuwa wasan zagaye na uku a cikin jerin wasannin neman gurbi guda biyar wanda zai ƙare a watan Disamba na shekara mai zuwa.

JERIN ‘YAN WASAN SUPER FALCONS 28 DA ZASU BUGA WASAN NEMAN GURBIN OLYMPICS DA COMOROS

Masu tsaron raga: Chiamaka Nnadozie (Brighton Hove & Albion, England), da Comfort Erhabor (Portsmouth Ladies, England) da kuma Christiana Uzoma (Edo Queens)

‘Yan wasan baya: Michelle Alozie (Chicago Stars, USA),  Shukurat Oladipo (AS Roma, Italy),  Farida Abdulwahab (Nasarawa Amazons), Glory Ogbonna (Besiktas JK, Turkey), Oluwatosin Demehin (SL Benfica, Portugal), Glory Edet (Bayelsa Queens),  Ashley Plumptre (Al-Ittihad Ladies, Saudi Arabia) da kuma Tumininu Adeshina (Edo Queens)

‘Yan wasan tsakiya: Christy Ucheibe (Al-Hilal, Saudi Arabia),  Joy Igbokwe (Nasarawa Amazons), Favour Nkwocha (FC Robo Queens), Fatimoh Solaty (Nasarawa Amazons), Suliat Abideen (Fenerbahce Ladies, Turkey), Toni Payne (Inter Milan, Italy) da kuma Jennifer Echegini (Paris Saint Germain, France)

‘Yan wasan gaba: Rasheedat Ajibade (Paris Saint Germain, France), Asisat Oshoala (Al-Hilal, Saudi Arabia), Flourish Sabastine (SL Benfica, Portugal), Shakirat Moshood (SCU Torreense, Portugal), Gift Monday (Washington Spirit, USA), Joy Omewa (BK Hacken, Sweden), Blessing Nkor (Dynamo Brest, Belarus), Oluwakemi Adegbuyi (Edo Queens), Janet Akekoromowei (SL Benfica, Portugal) da Uchenna Kanu (Cruz Azul Femenil, Mexico)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *