Wani matukin jirgin sama da ke tafiya daga Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa Isra’ila ya dabawa takwaransa wuka yayin da jirgin ke tsaka da tafiya a sararin samaniya
An ce rikici ya ɓarke tsakanin matuƙin jirgin da mataimakinsa, inda aka daba wa ɗaya daga cikinsu wuƙa.
Wani fasinja ya ce daga bisani wasu mutane suka kutsa cikin ɗakin matuƙan jirgin domin taimakawa wajen shawo kan ɗaya daga cikinsu, kafin su ɗaure shi.
Jirgin na kamfanin FlyDubai da ke kan hanyar zuwa Isra’ila ya aika da sanarwar gaggawa, sannan ya yi saurin saukowa daga tsayin ƙafa 33,000 zuwa ƙafa 17,000. Lamarin ya sa Isra’ila ta tura jiragen yaƙi domin fargabar yiwuwar sace jirgin.
- NNPC ta samu ribar Naira tiriliyan 7.2 a 2025
- Najeriya ta cika shekaru 66: Gwamnatin Tarayya ta ayyana 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu
- APC ta ba iyalan ’yan hakar ma’adinai 37 da suka mutu a Niger tallafin N52m
Wasu hotuna da bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, waɗanda kamfanin dillancin labara na AP ya wallafa, sun nuna wasu mutane biyu kwance a ƙasan jirgin cikin jini da raunuka.
Ana hango wasu mutane biyu suna ba su agajin gaggawa, yayin da wasu mutum biyu ke gadin ƙofar dakin matuƙan jirgin.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce fasinjoji da ma’aikatan jirgin da suka shiga tsakani sun “ceto rayuka da dama tare da hana lamarin rikidewa zuwa kazamin rikici.”
Ya ƙara da cewa Saudiyya ta kama wani matukin jirgi, sai dai hukumomin Saudiyya ba su bayyana sunansa ba a lokacin da rahoton ya fito.
Hukumomin filin jirgin saman kasa da kasa Prince Sultan bin Abdulaziz da ke Tabuk sun ce matukin ɗin jirgin da mataimakinsa sun samu raunuka.