Shugabannin ƙasashen Afirka da wasu manyan jami’ai sun isa garin Lamu da ke Kenya, domin halartar bikin aza harsashin ginin sabuwar matatar man fetur ta Dangote mai darajar dala biliyan 16.

Ana sa ran matatar, wadda hamshakin ɗan kasuwar Najeriya Aliko Dangote ke jagoranta, za ta zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan makamashi a Gabashin Afirka, tare da samar da man fetur da sauran kayayyakin mai ga Kenya da sauran ƙasashen yankin.

Shugaban Kenya William Ruto na cikin manyan shugabannin da suka halarci bikin, tare da wasu shugabannin ƙasashen Afirka ci har tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

Rahotanni sun ce matatar za ta kasance tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana. Ana sa ran aikin ginin zai ɗauki kusan watanni 40 kafin kammalawa.

Ana kuma sa ran aikin zai rage dogaron Kenya da sauran ƙasashen Gabashin Afirka kan shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje, musamman man fetur, dizal da man jiragen sama.

Matatar za ta samu damar amfani da ɗanyen mai daga wasu ƙasashen yankin, ciki har da Uganda da Sudan ta Kudu, sannan a rarraba kayayyakin da aka tace zuwa kasuwannin Kenya da sauran ƙasashen Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *