Rundunar Operation Fansan Yamma ta ce dakarunta sun ceto mata biyar da aka yi garkuwa da su a Jihar Katsina, tare da fatattakar harin ‘yan ta’adda da kuma kwato dabbobin da aka sace a Jihar Sokoto.
A Katsina, rundunar ta ce ta samu bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a yankin dajin Madaci da ke ƙaramar hukumar Sabuwa, inda dakarunta suka yi gaggawar kai farmaki tare da tare masu laifin.
Matakin ya haifar da rudani a sansanin ‘yan ta’addan, lamarin da ya ba rundunar damar ceto mata biyar, ciki har da wata uwa da jaririnta, da kuma wasu ƙananan yara da matasa daga ƙananan hukumomin Danja da Funtua.
- Shugabannin Afirka sun halarci bikin fara aikin matatar man Dangote ta dala biliyan 16 a Kenya
- Matukin jirgi ya daba wa abokin aikinsa wuƙa a jirgin FlyDubai
An ce an miƙa waɗanda aka ceto ga shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Musa, domin haɗa su da iyalansu.
Rundunar ta kuma ce dakarunta na ci gaba da sintiri a yankin domin hana ‘yan ta’adda sake samun damar gudanar da ayyukansu.
A Jihar Sokoto kuwa, dakarun Bataliya ta 248 ta leƙen asiri sun fatattaki wani harin ‘yan ta’adda a ƙauyen Badiya da ke ƙaramar hukumar Shagari.
Bayan samun bayanan sirri kan wasu mutane da ake zargin suna da hannu a ayyukan ta’addanci, dakarun sun tunkare su da ƙarfin da ya tilasta musu tserewa, inda suka bar garken dabbobin da suka sace.
Dakarun sun ce an mayar da dabbobin ga masu su a wani taƙaitaccen biki da shugaban ƙaramar hukumar Shagari da hakimin yankin suka jagoranta, domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’ummar yankin.