Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa wasu sassan ƙasar na iya fuskantar ambaliyar ruwa mai mai tsanani tsakanin 1 zuwa 10 ga Oktoban 2026.
NiMet ta ce jihohin da ke da matsakaicin yiwuwar fuskantar ambaliyar sun haɗa da Taraba, Benue, Ondo, Edo, Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa.
Hukumar ta kuma sanya Adamawa, Nasarawa, Kogi, Ekiti, Osun, Lagos, Enugu, Anambra, Ebonyi, Imo, Abia da Abuja cikin yankunan da ke da ƙarancin yiwuwar fuskantar ambaliyar a wannan lokacin.
- Dakarun Operation Fansan Yamma sun ceto mata biyar da aka sace a Katsina
- Shugabannin Afirka sun halarci bikin fara aikin matatar man Dangote ta dala biliyan 16 a Kenya
NiMet ta ce ci gaba da ruwan sama da ake yi, da cunkoson ruwa a ƙasa, da yawaitar kwararar ruwa, da kasancewar wasu wurare a ƙasa ko kusa da koguna na iya ƙara haɗarin ambaliya, musamman a yankunan kudancin ƙasar.
Hukumar ta shawarci jama’a da su riƙa bin hasashen yanayi da gargadin hukumomin da abin ya shafa, tare da guje wa tuki ko tafiya a wuraren da ruwa ya mamaye.
Ta kuma buƙaci hukumomin agaji su ƙara sanya ido da kuma tanadar da kayan aikin gaggawa a wuraren da aka gano suna cikin haɗari.
NiMet ta ce ambaliyar na iya haifar da cunkoson ababen hawa, da katsewar hanyoyi, da lalacewar tituna da gadoji, da lalacewar amfanin gona, da katsewar wutar lantarki da sadarwa, da kuma ƙara haɗarin yaɗuwar cututtukan da ruwa ke ɗauka.