Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya tabbatar da cewa daga yanzu za a riƙa gudanar da babban taron Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) duk shekara, domin ƙarfafa haɗin kai, shawarwari da daidaita ayyukan shugabannin Musulmi a faɗin ƙasar.
Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci babban taron majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis, 1 ga Oktoban 2026, a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce taron zai samar da wata muhimmiyar dama ga shugabannin Musulmi wajen tattauna batutuwan da suka shafi addini da ci gaban ƙasa.
- Dakarun Operation Fansan Yamma sun ceto mata biyar da aka sace a Katsina
- NiMet ta yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 21 na Nigeria
Sarkin ya bayyana cewa ba a gudanar da babban taron majalisar ba tsawon shekaru bakwai saboda wasu ƙalubale, sai dai an gudanar da taron babban kwamitin gudanarwa domin duba batutuwan da suka rage da kuma neman hanyoyin magance su.
Sarkin Musulmi ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kan Musulmi, yana kira gare su da su kiyaye ’yancin addini tare da marabtar duk wanda ya zaɓi shiga Musulunci da kansa, ba tare da tilastawa ba.
A yayin taron, Sarkin Musulmi ya yaba wa Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, kan kammala shekaru 10 na hidima mai inganci a matsayin Magatakardar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Ƙasa (JAMB).
Taron ya samu halartar sarakuna, limamai, malaman addinin Musulunci da sauran fitattun Musulmai daga jihohi 36 da Abuja, ciki har da Sarkin Bauchi da Etsu Nupe.