Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yaba wa al’ummar jihar kan jajircewa da imanin da suke da shi kan makomar Najeriya, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne bayan halartar faretin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai da aka gudanar a filin Mobolaji Johnson Arena da ke Onikan, Legas.

Gwamnan ya ce shekaru 66 muhimmiyar nasara ce, wadda ke wakiltar shekaru da dama na aiki tukuru da sadaukarwa daga al’ummomin da suka gabata da kuma ’yan Legas da ke ci gaba da yin aiki tuƙuru domin ci gaban ƙasa.

Ya jaddada cewa gina ƙasa aiki ne da ba ya ƙarewa, kuma yana buƙatar haɗin kan kowa domin cimma manufa guda.

Sanwo-Olu ya gode wa al’ummar Legas bisa juriyarsu da kuma ci gaba da amincewa da makomar da suke da ita tare, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin nata ɓangaren wajen gina Legas da za ta yi aiki ga kowa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *