Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa Masarautar Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujerun aikin Hajji 10,000 na shekarar 2027, lamarin da ya ɗaga adadin kunjerun da ƙasar za ta samu daga 50,000 zuwa 60,000.

NAHCON ta ce ƙarin kujerun 10,000 za a raba su tsakanin hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi da kamfanonin shirya aikin Hajji.

hukumar ta ce, za a bai wa hukumomin jihohi da hukumominsu 7,500, yayin da kamfanonin yawon buɗe ido guda bakwai da ke jagorantar harkar Hajji za su samu kujeru 2,500.

Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Najeriya bisa goyon baya da jagoranci da take bai wa harkokin Hajji da jin daɗin mahajjatan Najeriya.

Ya kuma gode wa Sarkin Saudiyya mai kula da Masallatan Harami guda biyu da gwamnatin ƙasar, musamman Ministan Hajji da Umrah, Dakta Tawfiq bin Fawzan Al-Rabiah, da mataimakinsa Dakta Abdul Fattah bin Sulaiman Mashat, bisa ƙarin kujerun da suka bai wa Najeriya.

Shugaban NAHCON ya ce ƙarin kujerun na nuna kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Saudiyya, tare da haɗin gwiwar ƙasashen biyu wajen sauƙaƙa aikin Hajji ga mahajjatan Najeriya.

Ya tabbatar da cewa za a raba ƙarin kujerun cikin adalci da gaskiya, tare da bin dokoki da ƙa’idojin Najeriya da Saudiyya.

Ya kuma jaddada aniyar hukumar na ganin aikin Hajji ya kasance mai sauƙin samu da araha ga ’yan Najeriya, tare da samar da ingantaccen tsari da kulawa ga mahajjata.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *