Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su sabunta ƙudurin gina ƙasa mai samar da dama, tsaro da ingantacciyar rayuwa ga kowa, yana mai cewa makomar Najeriya na hannun ’yan ƙasarta.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a saƙonsa na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya ce ranar ’yancin kai lokaci ne na yin tunani kan inda Najeriya take a yanzu, da inda take son zuwa da kuma matakan da ya kamata a ɗauka domin cimma wannan buri.

Ya ce duk da dumbin albarkatun ɗan Adam da na ƙasa da Najeriya ke da su, har yanzu miliyoyin ’yan ƙasa na fuskantar rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, yunwa da ƙarancin damar samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.

Kwankwaso ya jaddada cewa ya kamata Najeriya ta sauya daga tattalin arziƙin da ya fi dogaro da amfani zuwa tattalin arziƙin da ya fi mayar da hankali kan samarwa, tare da saka jari a matasa, ilimi, noma, masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa domin ƙirƙirar guraben aikin yi da damar samun wadata.

Ya kuma ce tsaro na daga cikin muhimman nauyin da ke rataye a wuyan gwamnati, yana mai cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin rayuwa, noma, kasuwanci da renon iyalansu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba.

Tsohon gwamnan ya ce a tsawon lokacin da ya yi a matsayin jagoran ƙungiyar ɗalibai, da ɗan majalisa, da minista da gwamna, ya kasance yana ganin cewa ya kamata a auna shugabanci da sakamakon da aka samu, ba alkawuran da aka yi kawai ba.

Kwankwaso ya ce Najeriya ba ƙasa ce da ba ta da matsaloli ba, amma kuma ba ƙasa ce da ba ta da hanyoyin magance matsalolinta ba, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su sabunta imaninsu da ƙasar tare da ƙudurin gina “sabuwar Najeriya mai inganci da wadata.”

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *