An gargadi ’yan jarida a Najeriya kan yadda amfani da kalaman ƙiyayya, da nuna wariya ta fuskar ƙabila da kuma wallafa bayanan da ba a tantance ba daga kafafen sada zumunta ke iya kawo cikas da rashin amincewar jama’a da kafafen yaɗa labarai.
An yi wannan gargadin ne yayin wani taron horaswa da Cibiyar Horas da ’Yan Jarida da Premium Times ta shirya tare da masana harkokin rikici-rikice, inda aka jaddada cewa aikin ɗan jarida a wannan zamani ya wuce kasancewa mai karɓa da isar da bayanai kawai, zuwa zama mai tantance sahihancin bayanan da ke yawo.
Masu horaswar sun yi gargaɗi musamman kan amfani da ƙabila wajen bayyana wanda ake zargi da aikata laifi, inda suka ce idan ba ta da alaƙa kai tsaye da labarin ko ba ta da hujjar da ta tabbatar da muhimmancinta, ambatonta na iya haifar da kallon wata ƙabila gaba ɗaya a matsayin masu aikata laifi.
- Sabuwar Najeriya mai inganci mai yiwuwa ce – Kwankwaso
- Najeriya a shekaru 66: Daga waya mai layi zuwa zamanin AI
Sun shawarci ’yan jarida da su tambayi kansu kafin wallafa labari ko asalin ƙabila ya dace da labarin, wace hujja ce ke goyon bayan ambatonsa, ko zai iya haifar da zargin ɗora laifi kan wata ƙungiya gaba ɗaya, da kuma ko labarin zai kasance haka idan wanda ake magana a kansa ya fito daga wata ƙabila.
A bangaren kafafen sada zumunta kuwa, masu horaswar sun ce samun labari a WhatsApp, X, TikTok ko wasu kafafe ba ya nufin cewa labarin ya zama sahihi. Sun kuma ja hankali kan haƙƙin mallaka, da sirrin mutane da kuma haɗarin ɓata suna idan kafar yaɗa labarai ta sake wallafa zargin da ba a tantance ba.
An kuma gabatar da dabarun tantance hotuna, da bidiyo da sauran abubuwan da masu amfani da kafafen sada zumunta ke wallafawa, ciki har da gano wanda ya fara wallafa bayanin, da tantance lokacin da wurin da aka ɗauki hoton ko bidiyon, da neman wasu hujjoji masu zaman kansu kafin amfani da shi a matsayin labari.
Masana sun kuma yi magana kan ƙalubalen da fasahar basirar kwamfuta ke haifarwa, musamman samar da hotuna, da muryoyi da bidiyoyi na bogi da ke iya kama da na gaskiya. Sun ce bai kamata ’yan jarida su dogara da manhajojin gano abin da AI ta samar kawai ba, domin waɗannan kayan aiki na iya yin kuskure.
A maimakon haka, an shawarci ’yan jarida su binciki asalin bayanin, da gano wanda ya fara wallafa shi, da tantance wurin da lokacin da aka samar da shi, sannan su nemi hujjoji daga wasu tushe masu zaman kansu.
Daga cikin kayan aikin da aka ba da shawarar wajen tantancewa akwai Google Reverse Image Search, da Google Lens, da InVID da FotoForensics.
Taron ya kuma jaddada muhimmancin aikin jarida mai kula da tasirin rahoto ga rikice-rikice, musamman a Najeriya inda al’amuran ƙabila, da addini, da siyasa da rikicin manoma da makiyaya ke iya sa labari ya haifar da tasiri mai girma fiye da abin da ya faru tun farko.
A ƙarshe, masana sun bayyana cewa saurin kai labari na iya ba kafar yaɗa labarai suna na ɗan lokaci, amma sahihanci da tantance gaskiya su ne ke gina amincewar jama’a na dogon lokaci.
