Dakarun Haɗin Gwiwar Sojojin Kasa na Kudu maso Gabashin Najeriya, Operation UDO KA, sun tarwatsa wata mafakar ’yan ta’adda tare da ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a Jihar Anambra.
Sojojin Bataliya ta 185, tare da haɗin gwiwar Anambra Vigilante Group, ne suka gudanar da aikin
Bayan sace mutane uku a yankin Osakwa General Area na ƙaramar hukumar Ihiala, dakarun Operation UDO KA tare da haɗin gwiwar Anambra Vigilante Group sun gudanar da aikin ceto tare da samun nasarar kubutar da mutanen.
- Sabuwar Najeriya mai inganci mai yiwuwa ce – Kwankwaso
- Najeriya a shekaru 66: Daga waya mai layi zuwa zamanin AI
- Najeriya ta samu ƙarin kujerun aikin Hajji 10,000
A ranar 1 ga Oktoba, 2026, sojojin sun sake gudanar da wani samame inda suka kama wani da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane.
A yayin binciken farko, wanda ake zargin ya bayar da bayanan da suka taimaka wajen gano sansanin ƙungiyar a Abator, ƙaramar hukumar Ogbaru, a hayin mashigar ruwan Isieke.
A yayin samamen, sojojin sun kwato bindigogin AK-47 guda biyu da harsashe, bindigogin Pump Action guda uku, da bindigogin Dane da aka ƙera a gida guda uku, harsasan 7.62mm NATO guda 62 da harsasan 7.62mm Special guda 149, baya ga harsashi guda biyu da wasu kayayyaki da ake zargin an tanade su ne domin kera na’urorin fashewa na gida (IEDs).