Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gargadi jama’a kan wani shafin bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa hukumar ta sake buɗe rajistar masu zaɓe ta intanet daga 28 ga Satumba zuwa 27 ga Oktoba 2026.
- Gwamna Kefas ya kira taron gaggawa kan tsaro a Taraba
- ’Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da fashi a Akure
INEC ta ce shafin ba shi da wata alaƙa da hukumar, tare da gargadin jama’a da kada su shiga cikinsa ko su shigar da bayanansu, domin hakan na iya jefa bayanan sirri cikin haɗarin satar bayanai ko amfani da su ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ta kuma bayyana cewa aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR) ya riga ya ƙare, kuma ba a gudanar da wata sabuwar rajistar masu zaɓe ta ƙasa baki ɗaya a halin yanzu.
INEC ta bukaci jama’a da su rika tabbatar da sahihancin bayanan zaɓe ta hanyoyin sadarwar hukumar kawai, musamman yayin da ake shirin babban zaɓen 2027.