Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar domin duba ƙarin matsalolin tsaro, da safarar miyagun ƙwayoyi da hare-haren da ba su da dalili da ake samun rahotonsu a sassan jihar.
Taron da aka gudanar a gidan gwamnatin TY Danjuma da ke Jalingo, ya haɗa shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka tattauna hanyoyin ƙarfafa matakan kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
- ’Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da fashi a Akure
- Gobara ta shafi shaguna 21 da mota a kasuwar kayan ɗaki ta Kugbo, Abuja
Gwamna Kefas ya nuna damuwa kan yadda laifuka da amfani da miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa, tare da jaddada buƙatar jami’an tsaro su kasance cikin shiri da kuma mayar da martani cikin gaggawa ga barazanar tsaro.
Ya kuma bukaci hukumomin tsaro su ƙara haɗin kai wajen magance matsalolin da suka shafi ayyukan haƙar ma’adinai.
Kefas ya ce tsaro nauyi ne da ya rataya a kan kowa, inda ya buƙaci shugabannin hukumomin tsaro su kasance masu gaskiya, jajircewa da aiki tare domin kare rayuka da dukiyoyi. Bayan jawabinsa, taron ya koma zaman sirri domin tattauna halin tsaron jihar da matakan da za a ɗauka.