Hukumar Fansho ta Sojoji ta fara aiwatar da sabon tsarin biyan fansho tare da biyan kuɗaɗen bashin baya ga tsoffin sojojin da suka yi ritaya.

Hukumar ta bayyana cewa an fara shigar da kuɗaɗen sabon tsarin fanshon da kuma bashin da ya tara cikin asusun ’yan fanshon tun daga ranar 2 ga Oktoba.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Squadron Leader Aliyu Mohammed, ya ce sauyin ya biyo bayan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ne, wanda ya haifar da buƙatar daidaita adadin fanshon da ake biyan tsoffin sojojin.

Hukumar ta gode wa ’yan fanshon bisa haƙuri da fahimtar da suka nuna yayin kammala tsarin, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da biyan fansho cikin lokaci da kuma inganta yadda ake gudanar da harkokin fansho.

Hukumar ta kuma yaba wa tsoffin sojojin bisa hidimar da suka yi wa Najeriya da irin sadaukarwar da suka yi wajen kare ƙasar, tare da neman ci gaba da ba ta haɗin kai wajen inganta harkokin fansho.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *