Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ƙananan hukumomi 16 na jihar da kamfanin Origin Tech Limited, domin gina hanyoyin karkara da za su haɗa manoma da kasuwanni.
Shirin na daga cikin matakan gwamnatin jihar na bunƙasa noma da samar da abinci, tare da buɗe hanyoyin zuwa gonaki, wuraren ajiya da cibiyoyin sarrafa amfanin gona.
- An kashe mutane 43 a Afirka ta Kudu kafin zaɓen ƙananan hukumomi
- Hukumar fansho ta sojoji ta fara biyan sabon tsarin fansho
Gwamnatin ta ce ta samar da tare da gwada kayan aikin noma da na gina hanyoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 16.
Gwamna Kefas ya ce haɗin gwiwar ba wai samar da kayan aiki kawai ya tsaya ba, har da tabbatar da yadda za a tura su wuraren da suka fi buƙata da kuma kula da su yadda ya kamata.
Ya kuma buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi su yi aiki tare da al’ummominsu domin jawo masu zuba jari a harkar noma.
A cewar Kwamishinan Noma da Samar da Abinci, Farfesa Nicholas Oliver Nemesan, shirin zai mayar da hankali kan noma, da sarrafa amfanin gona, da ban ruwa, da tara amfanin gona da kuma sarrafa shi.
Ya ce, hanyoyin karkarar kuma za su taimaka wajen sauƙaƙa kai amfanin gona zuwa kasuwanni da cibiyoyin ajiya da sarrafawa.
Shirin ya kuma ƙunshi bunƙasa kiwo da kafa cibiyoyin noma na musamman, inda Origin Tech ta ce an riga an samar da cibiyoyin noma guda shida tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar.