Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta rairayi ta Najeriya, Abdullahi Isa, ya yabawa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) bisa shirya wasannin sada zumunta guda biyu da Senegal, yana mai bayyana wasannin a matsayin muhimman shirye-shirye gabanin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta rairayi na nahiyar Afirka da za su kara da Ghana.

Sand Eagles za ta kara da Senegal, wadda ke riƙe da kambun zakarun Afirka, a wasanni biyu a jere da za a gudanar a Murtala Muhammed Square da ke Kaduna, ranar Asabar da kuma Litinin.

Isa ya ce yana sa ran wasannin za su taimaka wa ‘yan wasansa wajen dawo da ƙwarewar fafatawa da kuzarin gasa, gabanin muhimmiyar fafatawarsu da tawagar Black Sharks ta Ghana a wasannin neman gurbin shiga gasar nahiya.

Kocin ya nuna godiyarsa ga NFF bisa gayyatar Senegal zuwa Najeriya, tare da godewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal bisa amincewa da gayyatar.

Isa ya kuma bayyana jin daɗinsa da samun damar gwada ‘yan wasansa akan Senegal, wacce ta kafa kanta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da suka fi ƙarfi a ƙwallon rairayi a Afirka.

Shi ma kocin Senegal, Med Jean Sylla, ya ce wasannin sada zumuncin za su amfani tawagun biyu, yayin da suke shirye-shiryen wakiltar ƙasashensu a wasannin nahiyar Afirka.

Senegal za ta yi amfani da waɗannan wasanni biyu a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryenta na Gasar Ƙwallon Rairayin ta Afirka ta 2026, wadda za ta karɓi bakunci daga ranar 7 zuwa 15 ga Nuwamba, a matsayinta na mai riƙe da kambun gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *