Shugabar Ƙungiyar Matan Jami’an Sojin Najeriya (NAOWA), Dr Safiyyah Hassan Shaibu, ta kai tallafi da agaji ga wasu daga cikin iyalan sojoji a Kaduna, a wani mataki na ƙarfafa jin daɗi da walwalar iyalan sojoji.
A yayin ziyarar, Dr Shaibu ta zagaya wasu cibiyoyin NAOWA da suka haɗa da makarantu da cibiyar koyar da sana’o’i, inda ta yaba wa malamai da ma’aikata bisa jajircewarsu wajen ilimantarwa da tallafa wa iyalan sojoji tare da ba su kyautar kuɗi da kayan tallafi.
- Gwamnatin Tarayya na sa ran samar da ayyuka 10,000 daga kowanne babban mayanka
- Rundunar Sojin Sama ta karɓi sabbin jirage masu saukar ungulu guda biyu
Shugabar NAOWA ta kuma gana da zawarawan sojojin da suka rasu wajen gudanar da ayyukansu, inda ta mika musu tallafin kuɗi da kayan agaji, tare da tabbatar musu da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da tallafa musu.
Haka kuma, ta yaba wa matan sojojin Najeriya (NASWA) bisa juriyarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen kula da iyalansu yayin da mazajensu ke gudanar da ayyukan tsaron ƙasa.
NAOWA ta ce matakan na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da hangen nesanta na gina ƙungiya mai haɗin kai da ƙirƙire-ƙirƙire, wadda za ta taimaka wa iyalan sojoji wajen dogaro da kai da samun ingantacciyar rayuwa.