Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta karɓi sabbin jirage masu saukar ungulu guda biyu kirar H125 daga kamfanin Airbus Helicopters, a wani mataki da zai ƙara mata ƙarfin gudanar da ayyukan sama.
- Gwamnatin Tarayya na sa ran samar da ayyuka 10,000 daga kowanne babban mayanka
- Mutane 20 sun mutu a hatsarin mota a Plateau
An kammala karɓar jiragen ne a ranar 2 ga Oktoba a sansanin 355 Rotary Wing da ke Ikeja, Legas, inda aka sanya hannu kan takardun karɓar jiragen a madadin Rundunar Sojin Sama da kamfanin Airbus Helicopters.
Rundunar ta ce sabbin jiragen za su ƙara mata damar samar da tallafin sama cikin gaggawa a wuraren da ake buƙata, yayin da aka sake haɗa su a Najeriya tare da tallafin ƙwararrun Airbus.