Mutane 20 sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyar Hawan Kibo zuwa Jos, a Jihar Plateau, ranar Juma’a 2 ga Oktoba 2026.
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce mutane 25 ne hatsarin ya rutsa da su, inda biyar suka samu raunuka.
Motoci huɗu ne suka yi hatsarin, ciki har da babbar motar ɗaukar kaya, da Toyota Corolla, da motar bas ta Yankari Express da babur.
- Taraba ta rattaba hannu kan yarjejeniyar gina hanyoyin karkara a jihar
- An kashe mutane 43 a Afirka ta Kudu kafin zaɓen ƙananan hukumomi
Rahoton farko ya nuna cewa lalacewar birki da kuma rasa iko da abin hawa na daga cikin abubuwan da ake zargi sun haddasa hatsarin.
An kai waɗanda suka jikkata asibitoci domin samun kulawa, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka mutu ɗakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH).
Kwamandan Hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, tare da umartar ƙungiyar binciken haɗurra ta hukumar da ta gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya faru.
Hukumar ta kuma yi kira ga masu ababen hawa, musamman masu motocin haya da manyan motoci, da su tabbatar da lafiyar motocinsu, kula da birki, guje wa gudun wuce gona da iri da kuma bin ƙa’idojin tsaro kafin fara tafiya.