Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa goyon baya gabanin babban zaɓen 2027.
Gwamnan ya yi kiran ne a yayin taron Kadiriyya Maukibi da aka gudanar a Kano, wanda ya haɗa manyan malamai, ’yan siyasa da sauran manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar.
- APC ta ƙaddamar da gangamin neman kuri’u a Arewa ta Tsakiya
- NAOWA ta tallafa wa malaman makarantu, da matan jami’an soja a Kaduna
Taron ya kuma kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da zaman tare, yayin da aka ƙaddamar da sabon dandamalin Maukibi da gwamnatin Kano ta gina, wanda wakilin Shugaba Tinubu, Ibrahim Kabir Masari, ya ƙaddamar.
Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, da tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, na daga cikin manyan ’yan siyasar da suka halarci taron tare da gabatar da jawabai.