Daga Ibrahima Yakubu
Yayin da duniya ke bikin Ranar Dabbobi ta Duniya a ranar 4 ga Oktoba, 2026, ana ƙara jan hankali kan babbar barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa ga rayuwar dabbobi da kuma muhallin da suke dogaro da shi.
Ibrahima Yakubu, Shugaban Sashen Sadarwa da Dabaru na African Climate Reporters, ya ce sauyin yanayi na ƙara zama babbar barazana ga dabbobin daji da na gida.
Ya yi gargadin cewa hauhawar yanayin zafi, tsawaitar fari, ambaliyar ruwa mai tsanani, gobarar daji da sauye-sauyen yanayin ruwan sama na haifar da mawuyacin yanayi ga rayuwar dabbobi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, ya bayyana cewa a faɗin Afirka, nau’o’in dabbobin daji da dama suna dogaro da dazuzzuka,da filayen ciyawa, da dausayi, da koguna da sauran muhallai domin samun abinci, ruwa da mafaka.
Yayin da sauyin yanayi ke lalata ko sauya yanayin waɗannan muhalli, da dabbobi na ƙara tilastuwa yin doguwar tafiya domin neman abinci da ruwa, lamarin da ke jefa su cikin ƙarin haɗari.
Tsananin zafi na iya janyo wa dabbobi matsananciyar gajiya sakamakon zafi, da rashin ruwa har ma da mutuwa, yayin da dogon lokaci na fari ke lalata ciyayi tare da rage samun ruwa. Ambaliyar ruwa da gobarar daji kuma na iya lalata wuraren haihuwa, gad wuraren da dabbobi ke yin ƙwai da kuma muhallan da suke rayuwa, abin da ke rage wuraren da nau’o’in dabbobin da ke cikin haɗari za su iya rayuwa.
- Kocin tawagar Kwallon rairayi ta Najeriya ya yabawa Hukumar NFF kan wasan Gwaji da Senegal
- Najeriya ta samu tikitin shiga Gasar masu buƙata ta musamman ta Duniya ta 2027
- Gasar Olympics ta 2028: Eguavoen ya gayyaci Ajibade da wasu ‘yan wasa 27
Sauyin yanayi na kuma kawo cikas ga ƙaura, da haihuwa da tsarin neman abinci na dabbobi. Sauye-sauyen yanayin zafi da yanayin damina da rani na iya shafar lokacin da dabbobi ke yin ƙaura, da haihuwa ko neman abinci. Ga nau’o’in dabbobin da tuni ke fuskantar barazanar lalacewar muhalli, da farautar su ba bisa ƙa’ida ba, da gurɓacewar muhalli da sauran ayyukan ɗan Adam, da sauyin yanayi na iya ƙara tura su kusa da ƙarewa.
Yakubu ya jaddada cewa illolin ba su tsaya ga dabbobin daji kaɗai ba, domin dabbobin gida da na kiwo su ma na ƙara fuskantar matsanancin zafi, ƙarancin ruwa, raguwar wuraren kiwo da cututtukan da sauyin yanayi ke ƙara yaɗawa. Waɗannan matsaloli na iya yin barazana ga rayuwar al’ummomin da suka dogara da dabbobi wajen samun abinci da kuɗin shiga.
Ya yi kira da a ƙarfafa aikin jarida kan sauyin yanayi da muhalli, domin wayar da kan jama’a game da alaƙar da ke tsakanin sauyin yanayi, da rayuwar dabbobi da kare muhalli.
A cewarsa, ’yan jarida na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kawo rahotanni kan ɓacewar muhallan dabbobi, da raguwar hanyoyin samun ruwa da sauye-sauyen halayen dabbobin daji da sauran barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa, tare da bayyana hanyoyin magance matsalolin da za su taimaka wajen kare nau’o’in dabbobin da ke cikin haɗari.
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci, da ƙungiyoyin kare muhalli, da al’umma da ƙungiyoyin muhalli da su ƙara ƙoƙarin farfaɗo da wuraren da muhalli ya lalace da kare dazuzzuka da dausayi, da inganta tsarin kula da ruwa da rage ayyukan da ke haddasa sauyin yanayi.
Yayin da duniya ke bikin Ranar Dabbobi ta Duniya, Yakubu ya ce bai kamata bikin ya tsaya ga murnar dabbobi kawai ba. A maimakon haka, ya kamata ranar ta zama abin tunatarwa cewa rayuwar dabbobi ta dogara matuƙa ga lafiyar duniyar da muke rayuwa a cikinta.
Kare dabbobi daga illolin sauyin yanayi na nufin kare muhallansu; kare tsarin halittun muhalli da kuma kare makomar rayuwa baki ɗaya.