Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama mutum biyu bisa zargin hada baki, da hana jami’an gwamnati gudanar da aikinsu, da cin zarafin ’yan sanda da kuma lalata kayan gwamnati.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Oktoba a Yelwa Road, Bauchi, lokacin da jami’an Operation Velvet suka dakatar da wata mota domin duba takardunta.
- Musawa ta bai wa Tinubu hoton da ta zana shi da mahaifiyarsa
- SERAP ta bukaci a yi bincike kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan 94.4 na man fetur
A cewar ’yan sandan, mutanen biyu sun ki bayar da takardun motar tare da cin zarafin jami’an, har aka tsaga rigar wani Sajan.
Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya gargadi jama’a da su mutunta jami’an tsaro yayin da suke gudanar da ayyukansu bisa doka.