Tawagar ƙwallon ƙafar rerayi ta Najeriya, wato Sand Eagles, ta yi na mijin ƙoƙari a wasan sada zumunta na farko da ta buga da zakarar nahiyar Afirka na yanzu, wato Senegal, a wasan da suka buga a Kaduna a ranar Asabar, duk da ta sha kaye da ci 4-6.

Wasan wadda aka buga a filin wasa na Murtala Muhammed Square ya kasance fafatawa mai matukar nishaɗantarwa.

Senegal ce ta fara zura ƙwallo ta hannun Laye Diagne amma Najeriya ta hanzarta daidaita wasan ta hannun Abdullahi Hassan.

Sauran ƙwallayen Senegal sun zo ne ta hannun Mamadou Sylla (wadda ya ci ƙwallaye uku), da Ninou Jean-Paul Diatta, da kuma Asane Ba.

Dan wasa Abdullahi Hassan ne ya zura dukkan ƙwallaye huɗu da Najeriya ta ci, inda ya lashe lambar yabo na gwarzon ɗan wasa bisa ƙoƙarin da ya yi.

Ƙasashen biyu za su sake haɗuwa a wasa ta biyu na sada zumunta a safiyar ranar Litinin, a nan filin wasa na Murtala Muhammed Square, da ke Kaduna.

Sand Eagles ta na  amfani da wasannin sada zumunta ne a matsayin wani bangare na shirye-shiryenta na wasan neman shiga Gasar Cin Kofin Afirka ta ƙwallon ƙafar rerayi da za ta yi da Ghana a wannan watan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *