Tyson Fury da Anthony Joshua

Tyson Fury ya shirya gayyatar Shugaban Amurka, Donald Trump, ya raka shi zuwa dandalin wasan damben boxing a babban karawa da aka dade ana jira da Anthony Joshua.

“Tabbas zan mika wannan tayin ga tsohon abokina, kuma za mu ga ko zai samu damar zuwa,” in ji shi.

“Wataƙila hakan ba zai yiwu ba saboda halin da yake ciki a yanzu, na kasancewarsa Shugaban Amurka.”

Fury da Joshua, dukkansu tsofaffin zakarun duniya ne, sun kasance abokan hamayya shekaru da yawa kuma a karshe za su kece raini a ranar 11 ga Disambar wannan shekara a Cardiff.

‘Yan wasan biyu dukkannin su ‘yan Birtaniya ne, kuma a karon farko cikin wannan mako sun haɗu a taron manema labaru.

Fury ya ce ya na son Shugaban Amurka Trump ya shiga cikin tawagarsa zuwa dandalin wasan damben da za su yi a filin wasa na Principality Stadium mai daukar mutane 80,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *