Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa domin girmama jami’an Sojin Sama na Najeriya da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin soji a Igbokoda, Jihar Ondo.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin sauke tutocin Najeriya zuwa rabin sanda a faɗin ƙasar yayin zaman makokin, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga Rundunar Sojin Najeriya da ƙasa baki ɗaya.
Tinubu ya ce jami’an Sojin Sama na sadaukar da rayukansu wajen kare Najeriya, yana mai cewa ba za a manta da sadaukarwar da suka yi ba.
- NEMA ta tura tawagar fasaha wurin hatsarin jirgin NAF a Ondo
- NAF ta fitar da sunayen ma’aikata 25 da hatsarin jirgin sama a Ondo ya rutsa da su
Ya kuma umarci Rundunar Sojin Sama da ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin tare da ɗaukar matakan da za su hana sake faruwar irin wannan lamari.
Jirgin ATR-42 ɗin ya yi hatsarin ne a kusa da wani sansanin sojin ruwa da ke yankin Igbokoda, yayin da yake kan hanyar tafiya daga Benin zuwa Legas. Jirgin na ɗauke da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai.
Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya gafarta musu, Ya kuma ba iyalansu, ’yan uwansu da Rundunar Sojin Sama haƙurin jure wannan babban rashi.