Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana alhininsa kan hatsarin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) da ya yi sanadin mutuwar mutane a Igbokoda, Jihar Ondo.
Atiku ya ce abin da ya faru babban bala’i ne, musamman ganin cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai jami’an sojoji da ’yan uwansu.
- NAF ta fitar da sunayen ma’aikata 25 da hatsarin jirgin sama a Ondo ya rutsa da su
- Matawalle ya yi alhinin rasuwar jami’an NAF da ma’aikatan jirgin da suka mutu a hatsarin Ondo
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, Rundunar Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro, tare da addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya ba iyalansu da sauran ’yan Najeriya ƙarfin jure wannan babban rashi.
Hatsarin ya faru ne da wani jirgin ATR-42 na NAF da ke kan aikin yau da kullum daga Benin zuwa Lagos. Rundunar ta ce babu wanda ya tsira, yayin da aka fara bincike domin gano musabbabin hatsarin.