Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Sakataren Janar na Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Najeriya, Malam Nafiu Baba-Ahmed, wanda ya rasu a safiyar Talata.
A cikin saƙon ta’aziyyar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen jagoran addini da ma’aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa Musulunci da Najeriya.
Shugaban ya ce Baba-Ahmed ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da bayyana matsayar Majalisar Ƙoli ta Shari’a kan batutuwan ƙasa, tare da bayar da gudunmawa wajen inganta fahimtar juna, sake farfaɗo da ɗabi’un kirki da kuma tabbatar da adalci a cikin al’umma.
- Matawalle ya yi alhinin rasuwar jami’an NAF da ma’aikatan jirgin da suka mutu a hatsarin Ondo
- Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki bayan rasuwar jami’an Sojin Sama
Tinubu ya kuma tuna da dangantakarsa da marigayin tun kafin zaɓen 2011, inda ya ce Baba-Ahmed ya kasance mai ba shi shawarwari da goyon baya a wasu lokuta, musamman a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga shugabanni da mambobin Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Najeriya, iyalan Baba-Ahmed, gwamnatin da al’ummar Jihar Kaduna, da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Tinubu ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya shigar da shi Aljannar Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa da al’ummar Musulmi ƙarfin gwiwar jure wannan rashi.