Najeriya ta ƙaddamar da sabon tsarin adireshin dijital wato National Digital Alphanumeric Postcode System, wani sabon tsarin da NIPOST ta samar domin bai wa wurare da gine-gine a faɗin ƙasar wata lamba ta dijital da za ta sauƙaƙa gano su.
Tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙa isar da kaya da wasiku, ayyukan agajin gaggawa, harkokin kasuwanci da sauran ayyukan da ke buƙatar a iya gano ainihin inda mutum, kamfani ko wata cibiyar take.
- Rundunar ’yan sandan Bauchi ta kama wanda ake zargi da kisan wani mai shekara 46 bayan watanni uku
- Najeriya da Qatar sun tattauna ƙarin haɗin gwiwa, musamman samar da ayyukan yi
NIPOST ta buɗe Postcode Finder domin jama’a su duba lambar adireshinsu, su fara amfani da ita tare da adireshinsu a duk lokacin da suke bayar da bayanan wurin zama ko na kasuwanci.