Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya halarci wani babban taron kwanaki biyu kan sake fasalin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasashen Tafkin Chadi, MNJTF, domin ƙarfafa yaƙi da sabbin barazanar tsaro a yankin.
An gudanar da taron ne a Kwalejin Tsaro ta Ƙasa, National Defence College, da ke Abuja, ƙarƙashin taken: “Sake fasalin MNJTF domin tinkarar sauye-sauyen barazanar tsaro a yankin Tafkin Chadi yadda ya kamata.”
Taron ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen yankin, da inganta ayyukan MNJTF, da musayar bayanan sirri da kuma samar da hanyoyin da za su ba ƙasashen yankin damar mayar da martani cikin haɗin kai ga sauye-sauyen barazanar tsaro.
- Najeriya da Qatar sun tattauna ƙarin haɗin gwiwa, musamman samar da ayyukan yi
- Rundunar ’yan sandan Bauchi ta kama wanda ake zargi da kisan wani mai shekara 46 bayan watanni uku
Gwamna Kefas, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Laftanar Kanal a Rundunar Sojin Najeriya, ya shiga cikin tattaunawar da ta shafi barazanar ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP, da kuma sauran laifukan da suka ratsa iyakokin ƙasashe.
MNJTF na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi.
Rundunar na haɗa ƙasashen da ke cikin tsarin haɗin gwiwar, yayin da dakatarwar Nijar daga cikinta ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da ake ganin suna ƙara ƙalubalen tsaron iyakokin yankin.
Taron ya kuma zo ne a lokacin da ake ƙara kira ga ƙasashen yankin da su inganta musayar bayanan sirri, samar da kayan aiki da ƙarin tallafin da ake buƙata domin MNJTF ta iya tinkarar barazanar da ke sauyawa.
Hukumar Tarayyar Afirka ta ce, duk da nasarorin da aka samu wajen raunana ayyukan Boko Haram da ISWAP, har yanzu akwai gibi wajen samun isassun kayan aikin yaƙi, zirga-zirgar sojoji ta sama, na’urorin yaƙi da abubuwan fashewa, sadarwa da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan rundunar.
Ana sa ran tattaunawar za ta taimaka wajen sabunta haɗin gwiwar ƙasashen yankin da kuma samar da ingantaccen tsarin tsaro na bai ɗaya domin tinkarar barazanar ta’addanci da sauran laifukan da ke shafar yankin Tafkin Chadi.