Kotun daukaka kara da ke Kaduna ta ajiye hukunci kan karar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya shigar yana kalubalantar kin amincewa da bukatarsa ta beli da babbar kotun jihar ta yi.
Kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Onyekachi Aja Otisi ya saurari hujjojin lauyoyin El-Rufai da na Hukumar ICPC, amma kotun ba ta sanya ranar da za ta yanke hukuncin ba.
Lauyan ICPC, Ayodeji Adedipe, ya bukaci kotun ta yi watsi da karar, yana mai cewa El-Rufai ya gabatar da bukatun beli uku a babbar kotun Kaduna, kuma dukkansu an ki amincewa da su.
- Gwamna Kefas ya halarci taron ƙarfafa yaƙi da barazanar tsaro a Tafkin Chadi
- Gwamna Kefas ya halarci taron ƙarfafa yaƙi da barazanar tsaro a Tafkin Chadi
Sai dai lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, SAN, ya bukaci kotun ta soke hukuncin babbar kotun tare da bayar da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa laifukan da ake tuhumarsa da su ba na kisa ba ne kuma ana iya bayar da beli.
Erokoro ya kuma ce ci gaba da tsare El-Rufai na kawo cikas ga damar ganawa da lauyoyinsa da shaidu wajen shirya kare kansa.
Ya kuma yi nuni da cewa El-Rufai fitaccen dan adawa ne, tare da cewa lokacin da aka kawo kararrakin na da alaka da kusantar babban zaben 2027.
Yanzu dai hukuncin ya rage a hannun Kotun daukaka kara, wadda ba ta bayyana ranar da za ta yanke hukuncin ba.