Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da biyan Naira biliyan 10.32 na kuɗin sallamar aiki ga ’yan fansho 6,665 na gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan sabon biyan ya kai jimillar kuɗin sallamar aikin da gwamnatinsa ta biya tun bayan hawanta mulki a shekarar 2019 zuwa Naira biliyan 44.134.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na facebook, Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa ta tarar da bashin kuɗin sallamar aiki da ya haura Naira biliyan 21 lokacin da ta hau mulki a shekarar 2019, amma ta fara biyan bashin domin mutunta haƙƙin waɗanda suka yi wa gwamnati hidima tare da dawo musu da mutuncinsu.

Ya ce a halin yanzu, an kammala biyan dukkan bashin kuɗin sallamar aikin ma’aikatan gwamnatin jiha da ya taso har zuwa Disamban 2025, yayin da za a biya waɗanda bashinsu ya taso a shekarar 2026 a farkon shekarar 2027.

Gwamnan ya kuma bayyana fatansa na barin mulki ba tare da wani bashin kuɗin sallamar aiki da bai biya ba, da yardar Allah.

Ya gode wa ’yan fansho, Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da Ƙungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya bisa haƙuri da haɗin gwiwar da suka nuna.

Ya ƙara da cewa jin daɗin ’yan fansho na cikin abubuwan da gwamnatinsa ke ba muhimmanci.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *