Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun amince da ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tamowa, tare da shirin kafa wani asusun shiga tsakani na musamman domin ƙara kuɗaɗen yaƙi da yunwa da rashin abinci mai gina jiki a faɗin ƙasar.
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, yayin karanta matsayar da ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta cimma kan abinci mai gina jiki.
Wannan matsaya ta biyo bayan taron musayar ƙwarewa na kwanaki uku tsakanin Najeriya da Habasha, inda tawagar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ta nazarci hanyoyin da Habasha ke amfani da su wajen yaƙi da tamowa, musamman shirin Seqota Declaration.
- ADC ta bukaci ’yan Najeriya su karɓi katin zaɓensu, domin zaɓen 2027
- Wike ya zargi Amaechi da almundahana, ya yi barazanar hana shi kamfen a Ribas
A cewar gwamnonin, za a kafa Asusun Shiga Tsakani na Ƙasa kan Abinci Mai Gina Jiki domin ƙarfafa aiwatar da shirin Nutrition 774 Initiative, wanda aka tsara domin yaƙi da tamowa a dukkan ƙananan hukumomi 774 na Najeriya. Sun kuma amince da ƙarfafa samar da kuɗaɗen cikin gida da sa ido kan yadda ake amfani da su a matakin al’umma.
Gwamnonin sun kuma yi alƙawarin aiwatar da tsarin “Buri Ɗaya, Tsari Ɗaya, Kasafi Ɗaya” wajen tsara ayyukan abinci mai gina jiki, tare da amfani da bayanan ƙididdiga wajen tantance buƙatu, da rabon kuɗaɗe da auna nasarorin shirye-shiryen.
Sun bayyana cewa ya kamata a fara tsara buƙatun daga matakin unguwanni da al’ummomi, kafin haɗa su cikin tsare-tsaren ƙananan hukumomi, jihohi da na ƙasa. Haka kuma, za a faɗaɗa tsarin tantance nasarorin abinci mai gina jiki domin ya haɗa da ƙananan hukumomi da unguwanni.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Dakta Muyi Aina, ya ce gwamnatin tarayya za ta fara wani shiri na musamman a jihohi biyu da ke fama da matsananciyar matsalar ƙarancin tsawo sakamakon tamowa, kafin faɗaɗa shirin zuwa sauran jihohi.
Aina ya ce za a zaɓi jihohin ne bisa yawan yaran da ke fama da matsalar ƙarancin tsawo, sannan a tsara matakan da suka dace da buƙatunsu ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin lafiya, noma da sauran ɓangarori. Ya kuma bayyana cewa za a tsara tsarin haɗin gwiwar samar da kuɗaɗe da ma’aunan da za a riƙa amfani da su wajen auna ci gaba.
Ya ƙara da cewa ana shirin gudanar da tarukan bitar ci gaba bayan watanni uku, shida da tara, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, domin gano matsaloli da kuma tantance ko za a iya faɗaɗa shirin zuwa wasu jihohi.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce dole ne a mayar da alƙawuran da aka ɗauka zuwa ayyukan da za a iya aunawa, tare da fayyace nauyin da kowace gwamnati za ta ɗauka. Ya ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki tare da jihohi domin tabbatar da aiwatar da matakan da aka amince da su.
A nata jawabin, Ministar Lafiya ta Habasha, Dakta Mekdes Daba, ta yaba wa Najeriya bisa ƙoƙarin ƙarfafa yaƙi da tamowa, tare da bayyana shirinta na samar da taimakon ƙwarewa ga Najeriya.
Ta ce ya kamata a fara da matakan da za su samar da sakamako a bayyane, kafin faɗaɗa waɗanda suka yi nasara zuwa sauran wurare.