Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 29, bisa zargin haɗa baki da masu garkuwa da mutane wajen sace wani manomi wanda daga bisani aka kashe.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar a ranar 10 ga Oktoba, 2026, cewa jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ne suka kama wanda ake zargin a yankin Kuchi, kafin su miƙa shi ga ’yan sanda a sashen Sarkin-Pawa, bayan wasu mutanen da aka yi garkuwa da su kuma aka sako sun zarge shi da hannu a lamarin.

A cewar sanarwar, Godwin ya amsa zargin cewa a shekarar 2024 ya ɗauki wani mutum, wanda har yanzu yake tsere, domin shirya sace Jonah da nufin karɓar kuɗin fansa su raba tsakaninsu.

Sai dai an ce a ranar 26 ga Yuni, 2026, Mutumin da sauran mutanen da ake zargi sun kai hari ƙauyen Zawudna, suka kashe manomin tare da yin garkuwa da iyalansa da wasu mutane uku.

Rundunar ta ce masu garkuwar sun buƙaci a biya su Naira miliyan 2 da dubu 100 kafin sakin waɗanda aka sace.

Bincike ya kuma nuna cewa bayan mutuwar manomin, ana zargin mutumin ya karɓi gonarsa ya riƙa amfani da ita don amfanin kansa. A yanzu yana tsare a sashen binciken manyan laifuka na SCID da ke Minna, yayin da ake ƙoƙarin kama sauran waɗanda ake zargi.

A wani lamari daban, rundunar ta ce ta kama wasu mutane uku bisa zargin lalata kayan wutar lantarki da sata a yankunan Sarkin-Pawa da Barkin-Sale da ke Minna.

An kama wani matashi mai shekaru 25 a ranar 2 ga Oktoba, inda aka same shi da kebul mai sulke da ake zargin ya sace daga na’urar wutar lantarki.

Sanarwar ta ce ana zargin ya yi amfani da adduna da aka gyara kamar zarto wajen yanke kebul ɗin, da nufin sayar da shi ga masu sayen ƙarafa.

Haka kuma, a ranar 6 ga Oktoba, ’yan sanda sun kama wani mai shekaru 27 da wani mai shekaru 22, bisa zargin satar kebul na wutar lantarki da darajarsa ta haura Naira dubu 700 a Barkin-Sale.

A cewar rundunar, waɗannan mutane biyu sun amsa zargin cewa sun sace kebul ɗin ne da nufin sayar wa masu sayen ƙarafa.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan dukkan waɗanda aka kama, yayin da za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *