Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ceto Ahmed Zakka, matarsa da jaririnsu, waɗanda rahotanni suka ce an sace su a Jihar Kaduna.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan wani bidiyo mai tayar da hankali da aka ce na Ahmed Zakka ne, yana mai cewa lamarin ya sake nuna yadda rashin tsaro ke barazana ga rayukan ’yan Najeriya tare da wargaza zaman lafiyar iyalai.
A cikin saƙonsa, Atiku ya ce babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya kasance yana roƙon masu laifi domin ceton rayuwarsa ko ta iyalansa. Ya kuma bayyana damuwarsa kan kasancewar jariri cikin wannan mummunan hali.
- INEC ta cire Aminu Gwarzo na NDC daga jerin ’yan takarar gwamnan Kano
- INEC ta fitar da jerin ’yan takarar gwamnan Gombe, babu sunan Pantami
Ya buƙaci jami’an tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da sakin Ahmed Zakka, matarsa da ɗansu cikin ƙoshin lafiya, tare da ceto sauran ’yan Najeriya da ke hannun masu garkuwa da mutane.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma danganta matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa da jama’a ke fuskanta, yana mai cewa hauhawar farashin abinci, sufuri da sauran kayayyakin buƙata ta riga ta jefa iyalai cikin mawuyacin hali.
A cewarsa, rashin tsaro na ƙara tsananta talauci, kawo cikas ga hanyoyin samun abin dogaro da kuma ɗora wa iyalai nauyin kuɗi da na damuwa da ke da wahalar ɗauka.
Atiku ya yi kira ga gwamnati da ta wuce matakin yin alƙawura, ta samar da ingantattun matakan yaƙi da rashin tsaro, ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, kare al’ummomin da ke cikin haɗari da kuma wargaza hanyoyin sadarwar masu aikata laifukan.