Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC-PCC, ta yi Allah-wadai da dakile wani gangamin lumana mai taken “Tinubu Must Go” da rundunar ’yan sandan jihar Kano ta yi a cibiyar taruka ta The Avenue Event Center, inda ta bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Lahadi, ADC-PCC ta zargi ’yan sanda da tauye haƙƙin ’yan Najeriya na gudanar da taro cikin lumana da kuma bayyana ra’ayoyinsu.
- SERAP ta maka CBN a kotu kan zargin kashe sama da Naira tiriliyan 1.63
- Rahoton Bankin Duniya ya tabbatar da nasarar gyare-gyaren tattalin – Tinubu
- INEC ta cire Aminu Gwarzo na NDC daga jerin ’yan takarar gwamnan Kano
Gangamin, wanda Lauya Abba Hikima ya jagoranta tare da goyon bayan wasu matasa, ya samu tsaiko ne bayan jami’an ’yan sanda sun tare hanyoyin shiga cibiyar taron tare da zargin tsoratar da mahalarta.
Sai dai a martanin data mayar rundunar yansandan ta Jihar kano ta ce rashin tabbas game da yanayin tsaro ne ya sanya ta hana gudanar da taron da ƙungiyar da ke adawa da gwamnatin Shugaban kasa Tinubu wato TMG ta shirya a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema Labarai.
Ya ce ƙungiyar ba ta sanar da rundunar ’yan sanda game da shirya taron ba.
CP Bakori ya ƙara da cewa matakin dakatar da taron ya zama wajibi domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma