Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin rundunonin sojoji da sauran hukumomin tsaro, tare da inganta musayar bayanan sirri
Shaibu ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, yayin gabatar da lacca ta kammala horon kwas na 10/2026 a Kwalejin Yaƙi ta Sojojin Najeriya da ke Abuja.
- Kotu ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa Adeyemi kan hukumar bogi
- Ingantattun alkaluman tattalin arziki ba su rage talauci ba – Peter Obi
- NLC da NUT sun yi watsi da barazanar Wike kan hana ma’aikatan FCT albashi
Ya ce yanayin yaƙe-yaƙe na zamani na buƙatar hukumomin tsaro su haɗa ƙarfinsu da ƙwarewarsu domin samun nasara a ayyukan tsaro.
A cewarsa, faɗaɗa rundunar Sojojin Najeriya daga rundunoni takwas zuwa 12 na daga cikin dabarun ƙarfafa tsaro, faɗaɗa ayyukan soji a faɗin ƙasar da kuma inganta saurin mayar da martani ga barazanar tsaro.
Ya bayyana cewa manufar faɗaɗa rundunar ba wai ƙara yawan sojoji da rundunoni kaɗai ba ce, sai dai gina runduna mai ƙwarewa, juriya da kuma shirin tunkarar barazanar tsaro a kowane lokaci.