Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya ce dala biliyan ɗaya da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta amince a kashe wajen sayen kayan tsaro a lokacin da yake jagorantar sojoji, an miƙa su ne ga Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya, ba shi ko rundunonin soji ba.
Buratai ya bayyana hakan ne a taron Ƙungiyar Masu Rahoto kan Tsaro ta Najeriya da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda ya bayyana zarge-zargen cewa an karkatar da kuɗin a matsayin na siyasa da ƙeta.
Ya ce zarge-zargen sun fara bayyana ne a lokacin zaɓen shekarar 2019, lokacin da ’yan adawa suka yi iƙirarin cewa an karkatar da kuɗin domin ayyukan zaɓe.
- NLC da NUT sun yi watsi da barazanar Wike kan hana ma’aikatan FCT albashi
- Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya za ta faɗaɗa rundunoninta daga 8 zuwa 12
- Kotu ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa Adeyemi kan hukumar bogi
Ya ce ko dala ɗaya daga cikin kuɗin ba ta bi ta hannunsa ko asusun Sojin Ƙasa, Sojin Ruwa ko Sojin Sama ba. A cewarsa, Ma’aikatar Tsaro ce ta karɓi kuɗin tare da kula da dukkan tsarin sayen kayan tsaron.
Tsohon hafsan ya ce duk da cewa gwamnatin tarayya ta musanta zarge-zargen a lokacin, har yanzu takaddamar tana ci gaba da shafar martabar manyan hafsoshin tsaro. Ya kuma soki ma’aikatar bisa rashin fito wa fili ta yi bayani kan yadda aka raba kuɗin ko aka bayar da kwangilolin sayen makamai.
Buratai ya bukaci a samar da wata kafa ta yanar gizo domin nuna bayanai kan kwangilolin sayen kayan tsaro, da kamfanonin da aka bai wa kwangilolin da kuma lokacin kammala ayyukan, matuƙar hakan ba zai fallasa bayanan da suka shafi tsaron ƙasa ba.
Ya kuma ba da shawarar fitar da rahotannin lissafin alhaki duk bayan watanni uku, waɗanda za su taƙaita sakamakon shari’o’in kotunan soji da suka shafi take haƙƙin ɗan Adam da yadda ake gudanar da ayyukan soji, ba tare da tauye haƙƙin waɗanda ake zargi ko kawo cikas ga ayyukan tsaro ba.
Dangane da zarge-zargen take haƙƙin ɗan Adam da jami’an tsaro, Buratai ya ce duk zargi mai inganci ya kamata a gudanar da bincike a kansa, sannan a gurfanar da waɗanda aka tabbatar sun aikata laifi. Ya jaddada cewa sojoji ba su fi ƙarfin doka ba, yana mai cewa tsarin ladabtarwa a rundunar ya kamata ya kasance abin gaskatawa, mai gaskiya da kuma iya ɗaukar mataki a kan duk wanda ya aikata laifi.
A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce ba za a iya magance ƙalubalen tsaron Najeriya da ƙarfin soji kaɗai ba. Ya ce ana buƙatar ingantattun bayanan sirri, fasahar zamani da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’umma.
Ministan, wanda Darakta-Janar na Muryar Najeriya, Jibrin Ndace, ya wakilta, ya ce ayyukan soji suna da muhimmanci, amma dole ne a haɗa su da matakan magance abubuwan da ke sa ƙungiyoyin masu aikata laifi samun mambobi da barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Idris ya ce ajandar Shugaba Bola Tinubu ta Renewed Hope ta sanya tsaron ƙasa cikin manyan abubuwan da gwamnati ke mayar da hankali a kai. Ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin sabunta kayan aikin rundunonin tsaro, ƙarfafa ayyukan da ake gudanarwa bisa bayanan sirri da inganta sa ido da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
Ya kuma bayyana cewa a watan Agustan 2026, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin shirya cikakken rahoton tantance barazanar tsaro ta ƙasa da kuma wani shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar da za a riƙa sabuntawa, domin inganta haɗin kai, tsara abubuwan da suka fi muhimmanci da kuma jagorantar yadda za a raba albarkatu.
Ministan ya ƙara da cewa Tinubu ya amince da ƙarin albashi tsakanin kashi 30 zuwa 80 ga jami’an rundunonin tsaro, wanda aka fara aiki da shi a watan Satumbar 2026, a matsayin amincewa da sadaukarwar da suke yi.
Ya ce ya kamata matakan tsaro su haifar da sauyi da jama’a za su gani, ciki har da zaman lafiya a unguwanni da kan hanyoyi, kariya ga manoma da ’yan kasuwa, da kuma yanayin da yara za su iya zuwa makaranta ba tare da tsoro ba.
Dangane da rawar kafafen yaɗa labarai, Idris ya ce sahihan rahotanni da tantance bayanai cikin kulawa suna taimaka wa jama’a fahimtar halin tsaro tare da hana jita-jita haifar da fargaba ko kawo cikas ga ayyukan soji.
Sai dai ya jaddada cewa hakan ba yana nufin hana ’yan jarida bincika gwamnati ko hukumomin tsaro ba ne, yana mai cewa ya kamata su ci gaba da yin tambayoyi masu zurfi tare da mutunta bayanan da suka shafi sirrin ayyukan tsaro.