Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya ce ingantuwar wasu alkaluman tattalin arzikin Najeriya ba ta nuna cewa rayuwar ’yan ƙasar ta inganta ba, yana mai cewa har yanzu talauci, rashin aikin yi da rashin daidaiton tattalin arziki na ci gaba da addabar jama’a.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC kan yadda take bayyana nasarorin tattalin arziki, duk da wahalhalun da talakawa ke fuskanta.

Ya ce ya kamata a auna nasarar tattalin arziki ta fuskar raguwar talauci, da samar da ayyukan yi ga matasa da rage tazarar arziki tsakanin jama’a.

Ya ce ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na gwamnati, bunƙasar tattalin arziki da ingantuwar ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ba su isa a ce tattalin arziki ya daidaita ba, matuƙar jama’a ba za su iya samun abinci, kula da lafiya da ilimi ga ’ya’yansu ba.

Obi ya yi nuni da rahoton Bankin Duniya mai taken Beyond the Federal Purse: How Higher Revenues Reshaped State Priorities, inda ya ce gwamnatin tarayya ta kashe naira tiriliyan 7.7 wajen biyan kuɗin ruwa na basussuka a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026, daga Janairu zuwa Yuni.

A cewarsa, wannan adadi ya kai kusan kashi 124.2 cikin ɗari na kuɗaɗen shiga da suka kai naira tiriliyan 6.2 a wannan lokaci, lamarin da ya nuna cewa kuɗin ruwa na basussuka ya zarce kuɗaɗen shiga da kusan naira tiriliyan 1.5.

Ya tambayi dalilin da ya sa matsalar basussuka ke ƙara tsananta duk da ƙaruwa a kuɗaɗen shiga tun shekarar 2023.

Tsohon ɗan takarar ya kuma yi iƙirarin cewa duk da ƙaruwa a basussuka da kuɗaɗen shiga, an rage kashe kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa da kusan naira biliyan 700 a rabin farko na shekarar 2026.

Ya ce gwamnatin tarayya na kashe kuɗi wajen biyan ribar basussuka da ya ninka na ayyukan raya ƙasa sau 11, yana danganta hakan da abin da ya kira almubazzaranci, cin hanci da rashawa da rashin ƙwarewar gwamnati.

Obi ya ce bai kamata gwamnati ta dogara da alkaluman tattalin arziki kaɗai wajen bayyana nasarori ba, ba tare da la’akari da tasirin manufofinta ga rayuwar jama’a ba.

Ya kuma yi nuni da wani rahoton Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), wanda a cewarsa ya nuna cewa kusan ’yan Najeriya miliyan 140 na fama da talauci ta fannoni daban-daban.

Ya jaddada cewa ya kamata a tantance sauye-sauyen tattalin arziki bisa amfanin da suke kawowa ga jama’a, musamman talakawa da masu rauni.

A cewarsa, duk wani tsari da ke jefa jama’a cikin wahala ya kamata ya samar da sakamako mai ma’ana, wanda za a iya gani da auna shi.

Obi ya bukaci gwamnatin Tinubu ta sake duba manufofinta tare da mayar da hankali kan jin daɗin ’yan Najeriya, samar da ayyukan yi, rage talauci da rashin daidaito.

Ya ce ainihin nasarar tattalin arziki ita ce inganta rayuwar jama’a, ba kawai kyawawan alkaluma a takardu ba.

Ya kammala da cewa Najeriya na buƙatar tattalin arzikin da zai yi wa ’yan ƙasa hidima, tare da kawo ƙarshen talauci da samar da isassun ayyukan yi ga matasa.

Ya ce yana da yiwuwa a gina sabuwar Najeriya mai ɗorewar ci gaba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *