Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta buƙaci alƙalai a matakai daban-daban na kotuna da su rungumi sauye-sauye da amfani da fasahar zamani domin hanzarta shari’o’i da tabbatar da adalci.
Ta bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabin buɗe sabuwar shekarar shari’a ta 2026 zuwa 2027 a harabar Kotun Ƙoli da ke Abuja.
Kekere-Ekun ta ce karuwar yawan shari’o’in da ake gabatarwa a kotuna na buƙatar alƙalai su rungumi sabbin hanyoyin aiki da fasahar zamani domin sauƙaƙa gudanar da shari’o’i da rage jinkiri wajen yanke hukunci.
- ’Yan sandan Kano sun kama mutum huɗu, sun ƙwato motoci uku da aka sace
- Masu adawa a Indiya sun kai ƙara Kotun Ƙoli kan cire sunayen masu zaɓe
Da take nazarin ayyukan ɓangaren shari’a a shekarar da ta gabata, ta bayyana cewa an shigar da shari’o’i sama da 2,000 a Kotun Ƙoli, inda mafi yawansu suka shafi shari’o’in farar hula.
Haka kuma, yayin bikin rantsar da sababbin manyan lauyoyi 68 da aka ba muƙamin Babban Lauya a Najeriya (SAN), Babbar Jojin ta gargaɗe su da su guji yin kalaman da za su zubar da mutuncin kotuna da hukuncinsu a kafafen yaɗa labarai.
Ta jaddada muhimmancin kiyaye ƙa’idojin aikin lauya da mutunta hukumomin shari’a domin ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin shari’ar ƙasar.