Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhume-tuhume takwas da gwamnatin tarayya ta shigar kan Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da bayyana kansa a matsayin Darakta-Janar na wata hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).
Mai Shari’a Mohammed Umar ne ya dakatar da shari’ar ranar Litinin, bayan gwamnatin tarayya ta nemi a kawo ƙarshenta domin a sake gurfanar da wanda ake zargin a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT).
Babban Lauya Rotimi Oyedepo (SAN), wanda shi ne Daraktan Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya, ne ya gabatar da buƙatar a madadin gwamnati.
- Ingantattun alkaluman tattalin arziki ba su rage talauci ba – Peter Obi
- NLC da NUT sun yi watsi da barazanar Wike kan hana ma’aikatan FCT albashi
Ya shaida wa kotun cewa Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a ya sake nazarin fayil ɗin shari’ar Adeyemi da tuhume-tuhumen da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya shigar, inda aka gano wasu matsaloli.
Oyedepo ya bayyana cewa takardun da ake zargin Adeyemi ya ƙirƙira ko ya yi wa jabu yayin gudanar da ayyukan hukumar da ake zargin ta bogi ce, sun fi dacewa a gurfanar da shi a Babbar Kotun FCT maimakon Babbar Kotun Tarayya.
Matakin ya buɗe hanyar sake gurfanar da Adeyemi a wata kotu daban, amma dakatar da shari’ar a Babbar Kotun Tarayya ba yana nufin an wanke shi daga zarge-zargen ba.