Gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da ɗaukar yara ƙanana aiki a matsayin sojoji

An sanya Najeriya cikin jerin ne bisa rahoton shekara-shekara na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan safarar mutane na shekarar 2026, wanda ya yi nuni da ci gaba da ɗaukar yara ƙanana da amfani da su a matsayin mayaƙa daga ƙungiyoyin Boko Haram da ISIS-WA a cikin ƙasar.

Rahoton, wanda aka fitar ranar 11 ga Oktoba, ya ƙunshi abubuwan da suka faru daga 1 ga Afrilu, 2025, zuwa 31 ga Maris, 2026.

Najeriya tana cikin ƙasashe 14 da rahoton ya ambata, ciki har da Rasha, Iran, Sudan ta Kudu da Somaliya, waɗanda ake zargi da ɗaukar yara ƙanana ko amfani da su a matsayin sojoji.

Rahoton ya ce gwamnatocin ƙasashen da aka sanya cikin jerin za su fuskanci takaita wasu tallafin tsaro da lasisin kasuwancin kayan aikin soja a shekarar kuɗi ta gaba.

Dokar hana amfani da yara a matsayin sojoji ta Amurka, wato Child Soldiers Prevention Act (CSPA), ta haramta wasu nau’o’in taimakon soji, ciki har da shirin horas da jami’an soji na ƙasashen waje, tallafin kuɗin sayen kayan aikin soji, bayar da kayan aikin tsaro da suka rage, da kuma wasu ayyukan wanzar da zaman lafiya, duk da cewa akwai keɓancewa ga wasu shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *