Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan albashin sabbin ma’aikata 3,100 da aka ɗauka aiki a ma’aikatan gwamnati, bayan kammala tantance su domin tabbatar da sun halarci wuraren aikin da aka tura su.
Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Abdulkadir Ahmed, ne ya ƙaddamar da biyan albashin a wani taro da aka gudanar a ofishin sakatariyar gwamnati da ke Sokoto.
Ya ce ɗaukar ma’aikatan na daga cikin cika alƙawarin da Gwamna Ahmed Aliyu ya yi na samar da ayyukan yi ga matasa da sauran masu neman aikin yi a jihar.
- INEC da ECONEC sun amince da ƙa’idojin amfani da AI a zaɓe
- Magoya bayan APC sun gudanar da gangami a Legas domin nuna goyon baya ga Tinubu da Hamzat
Ya kuma buƙaci sabbin ma’aikatan su kasance masu zuwa aiki a kan lokaci, jajircewa da kuma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A cewar sanarwar da Daraktan yaɗa labarai na gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ɗauki ma’aikata sama da 8,000 a fannoni daban-daban cikin shekaru uku.
Daga cikinsu, 1,805 na ɓangaren lafiya ne, yayin da aka ɗauki jami’ai 2,747 a Rundunar Tsaron Al’umma ta Sokoto da kuma wasu 1,550 a Rundunar Marshals ta jihar.
Gwamnatin ta ce ɗaukar ma’aikatan ya gudana ne ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar masu neman aikin ba, domin bai wa duk wani ɗan asalin jihar da ya cancanta damar samun aiki.
Ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da shirye-shiryen koyar da sana’o’i da tallafa wa matasa da mata domin su dogara da kansu.