Wani likitan haƙora, Dakta Ridwan Kekere-Ekun, ya ce tsadar kayan aikin likitocin haƙora, da kayayyakin jinya da gudanar da asibitoci na hana ’yan Najeriya samun kulawar haƙora a kan lokaci.
Dakta Kekere-Ekun, wanda shi ne mataimakin daraktan lafiya na Babban Asibitin Apapa da kuma babban likitan haƙora na asibitin, ya bayyana hakan ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Litinin.
Ya ce yawancin kayan aikin likitocin haƙora da ake shigowa da su daga ƙasashen waje sun yi tsada sakamakon faɗuwar darajar naira, lamarin da ke ƙara kuɗin da marasa lafiya ke biya wajen samun magani.
- Peter Obi ya ce gwamnatin Tinubu na tsoratar da masu zuba jari a Najeriya
- Gwamnatin Sokoto ta fara biyan albashin sabbin ma’aikata 3,100
Likitan ya ƙara da cewa tsadar makamashi, musamman man fetur da dizal da asibitoci ke amfani da su wajen samar da wutar lantarki, na ƙara kuɗin gudanar da asibitoci, wanda daga bisani ake ɗora wa marasa lafiya ta hanyar ƙarin kuɗin magani.
Ya kuma danganta matsalar da ƙarancin tallafin da gwamnati ke bai wa asibitoci da kuma rashin cikakkiyar amincewar jama’a ga tsarin inshorar lafiya.
A cewarsa, rashin isasshen inshora na tilasta wa mutane biyan kuɗin ganin likita, gwajin hoto, magunguna da sauran jinyar haƙora daga aljihunsu.
Dakta Kekere-Ekun ya ce matsin tattalin arziki kan hana wasu marasa lafiya kammala gwaje-gwaje da jinyar da likitoci suka ba su shawara, inda ya ce wasu kan bar magani tun bai kammala ba, yayin da wasu ke zaɓar yin guda ɗaya daga cikin jinyoyi da dama da suke buƙata.
Ya yi gargaɗin cewa hakan na iya haifar da ƙarin matsalolin haƙora, kwantar da marasa lafiya a asibiti ba tare da shiri ba, tsawaita lokacin jinya da kuma buƙatar ƙarin gwaje-gwaje.
Ya ce jinkirta magani na iya sa a tura marasa lafiya wasu asibitoci ko ga ƙwararrun likitoci, tare da ƙara haɗarin rashin lafiya mai tsanani da mutuwa.
Likitan ya ce matsalar ta zama ruwan dare tsakanin marasa lafiyar da ke zuwa asibitin, inda wasu ke yawo daga asibiti zuwa wani domin neman wanda zai yi musu magani a farashi mai sauƙi.
Ya buƙaci gwamnati ta ƙara kuɗaɗen tallafi ga sassan kula da haƙora, ta rage harajin shigo da kayan aikin likitocin haƙora daga ƙasashen waje, tare da faɗaɗa tsarin inshorar lafiya domin rage kuɗin da marasa lafiya ke biya da kansu.
Ya kuma ba da shawarar ƙara wayar da kan jama’a kan kariyar lafiyar haƙora, gudanar da ayyukan wayar da kai a cikin al’umma, bayar da wasu ayyukan tsaftace haƙora kyauta da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ƙara da cewa rage kuɗin wutar lantarki ta hanyar tallafin lantarki da dizal, taimakon samar da janareta da amfani da hasken rana na iya rage kuɗin gudanar da asibitoci.