Wata mai zane da rubutun ƙawa daga ƙasar Azarbaijan, mai suna Tünzale Memmedzade, ta ɗauki tsawon shekaru uku tana rubuta Alƙur’ani Mai Girma baki ɗaya a kan wani yadi mai launin baƙi da ake iya hango ta bayansa.
Mawaƙiyar ta yi amfani da yadin alhariri mai tsawon mita 50 wajen rubuta ayoyin Alƙur’ani da hannunta, cikin ƙwarewa da haƙuri.
Rahotanni sun bayyana cewa ba ɗinkin rubutun ta yi ba, kamar yadda wasu bayanai da ke yawo a kafafen sadarwa suka nuna ba, a’a, ta yi amfani da tawada mai ɗauke da zinariya da azurfa wajen rubuta ayoyin.
- Sojoji sun kashe ’yan Lakurawa tare da ƙwace makamai a Sokoto
- Jami’ar Abuja ta haɗa gwiwa da GGI kan kare haƙƙin mata da koyar da dabarun kare kai
- Hauhawar farashi a Najeriya ya ragu zuwa kashi 14.63% a Satumba — NBS
An ce ta yi amfani da kusan mililita 1,500 na wannan tawada domin kammala aikin.
Memmedzade ta yi amfani da rubutun Alƙur’ani da Hukumar Kula da Harkokin Addini ta ƙasar Turkiyya, wadda aka fi sani da Diyanet, ta amince da shi.
Mawaƙiyar ta bayyana cewa a tarihi, an riƙa rubuta Alƙur’ani a kan abubuwa daban-daban, ciki har da fatun dabbobi da katako, amma ita ta zaɓi yin amfani da alhariri domin gabatar da cikakken Alƙur’ani a wata siga ta musamman.
Ta kuma yi nuni da cewa an ambaci alhariri a cikin Alƙur’ani Mai Girma.
Wannan aiki na musamman ya jawo hankalin mutane saboda yadda ya haɗa rubutun ƙawa na Musulunci da fasahar zane, tare da nuna irin haƙuri, ƙwarewa da jajircewar da ake buƙata wajen kammala irin wannan aiki mai girma.