Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka a Najeriya ya sake raguwa, inda ya kai kashi 14.63 cikin 100 a watan Satumba na shekarar 2026, daga kashi 15.39 cikin 100 da aka samu a watan Agusta.
Bayanan hukumar sun nuna cewa hauhawar farashin ya ragu da maki 6.35 idan aka kwatanta da kashi 20.98 da aka samu a Satumba na shekarar 2025.
A ma’aunin wata zuwa wata, hauhawar farashin ya tsaya a kashi 0.06 cikin 100 a Satumba, sabanin kashi 0.71 a watan Agusta.
- Taron AI ya jaddada buƙatar sa ido kan amfani da fasahar AI a zaɓen 2027
- Rundunar soji ta horas da ƙananan hafsoshi kan jagoranci
- Sojoji sun kashe ’yan Lakurawa tare da ƙwace makamai a Sokoto
A yankunan birane, bayanan NBS sun nuna cewa hauhawar farashin ya ragu da maki 12.58 idan aka kwatanta da kashi 28.48 da aka samu a Satumba na shekarar 2025.
A yankunan karkara kuwa, hauhawar farashin ya kasance kashi 12.46 a ma’aunin shekara zuwa shekara.
Hukumar ta kuma bayyana cewa matsakaicin hauhawar farashin kayayyaki a yankunan karkara na tsawon watanni 12 ya kai kashi 15.32 a Satumba.
Wannan ya yi ƙasa da kashi 25.67 da aka rubuta a Satumba na shekarar 2025.