Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun kashe wasu ’yan ta’addan Lakurawa tare da ƙwato makamai da babura biyar a yayin wani samame da suka kai sansaninsu da ke dajin Waria, ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Sanarwar da jami’in hulɗa da kafafen yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar 15 ga Oktoba, 2026, ta ce dakarun sun gudanar da aikin share daji ne bayan sun bi ta yankunan Alela, Bilange da Kandam zuwa dajin Waria.
- Majalisar Dattawa ta bukaci agajin gaggawa ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa
- Taron AI ya jaddada buƙatar sa ido kan amfani da fasahar AI a zaɓen 2027
Sanarwar ta bayyana cewa sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan, inda suka yi amfani da ƙarfin wuta, lamarin da ya tilasta wa maharan barin matsugunansu tare da tserewa cikin dajin.
Dakarun sun bi sawun waɗanda suka tsere, inda suka kashe wasu daga cikinsu. Sun kuma lalata sansanonin ’yan ta’addan da kayayyakin da suke amfani da su wajen rayuwa, tare da ƙwato makamai da babura biyar.
Rundunar ta ce dakarunta na ci gaba da gudanar da samame da sintiri a yankin domin hana ’yan ta’adda samun mafaka da damar gudanar da hare-hare, tare da ƙarfafa tsaron al’ummomin da ke kewaye.
Ta kuma yaba wa dakarun bisa jarumta da jajircewarsu, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa game da motsin mutane ko wasu abubuwan da suke zargi a yankunansu.