Jami’ar Abuja ta kulla haɗin gwiwa da ƙungiyar Guardian Girls International (GGI) domin ƙarfafa wayar da kan mata, ilimin tsaro da koyar da dabarun kare kai ga ’yan mata a Najeriya.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a yayin ƙaddamar da shirin Guardian Girls Nigeria (GGN), wanda aka gudanar a ofishin jakadancin Japan da ke Abuja ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi, ya sake tabbatar da goyon bayan jami’ar ga shirin, yana mai cewa manyan makarantu na da muhimmiyar rawa wajen gudanar da bincike, bunƙasa jagoranci da samar da yanayi mai aminci ga ’yan mata.

Jakadan Japan a Najeriya, Suzuki Hideo, ya yaba da shirin, inda ya jaddada muhimmancin wasannin yaƙi wajen ƙarfafa gwiwar ’yan mata da koya musu dabarun kare kansu.

Ya ce haɗin gwiwar zai kuma ƙara ƙarfafa dangantakar Najeriya da Japan ta fuskar ci gaba, al’adu da wasanni.

Shugaban GGI, Shin Koyamada, ya bayyana cewa manufofin shirin sun haɗa da amfani da wasanni da dabarun yaƙi wajen ƙarfafa mata, tare da yaƙi da cin zarafi bisa jinsi.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da shugabar Guardian Girls Nigeria, Ambasada Ruqayya Ahmed; wakiliyar asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) a Najeriya, Muriel Mafico; shugaban kwamitin wasannin Olympic na Najeriya, Injiniya Habi Gumel; da shugabar Guardian Girls Africa, Mary Obande.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *