Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki (PGF), Gwamna Hope Uzodimma na Jihar Imo, ya jagoranci gwamnonin jam’iyyar zuwa bikin rantsar da Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, domin fara wa’adinsa na biyu.

Uzodimma ya bayyana hakan ne a saƙon taya murna da ya fitar bayan rantsar da Oyebanji, wanda ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar.

Ya ce sake zaɓen Oyebanji na nuna yadda al’ummar Jihar Ekiti suka sake nuna amincewarsu da shugabancinsa da kuma manufofinsa.

Gwamnan na Imo ya bayyana kwarin gwiwar cewa Oyebanji zai ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da bunƙasa tattalin arzikin jihar, domin inganta walwala da ci gaban al’ummar Ekiti.

Uzodimma ya taya takwaransa murnar samun sabon wa’adin mulki, tare da yi masa fatan samun nasarar cika alƙawuran da ya ɗauka da kuma cimma muradun al’ummar jihar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *